(ABNA24.com) Wata sanarwa da ma’aikatar yada labaren kasar ta fiyar ta ce shugaban ya yi hakan ne bisa shawarwarin likitoci, da kuma bin ka’idodin dakile yaduwar cutar ta korona.
An sanar da cewa akalla daya daga cikin wadanda ke kusa da shugaban ya kamu da cutar COVID-19 a ranar Juma’a.
Ya zuwa yanzu dai, gwajin da aka wa shugaban kasar ya nuna cewa ba ya dauke da cutar, amma duk da haka ya dauki wannan matakin na killace kansa.
A tsawon lokacin da zai kasance a killace, Shugaban zai ci gaba da gudanar da ayyukansa daga fadar gwamnatin kasar, da ke birnin Accra.
A ranar Juma’a ne sakataren gwamnatin kasar mai lura da harkokin kasuwanci da masana’antu, Kingsley Ahenkora, wanda gwajin da akayi masa ya tabatar ya harbu da cutar, ya sanar da yin murabus daga aiki, saboda karya dokar kebance kasan, ta hnayar gudanar da yakin neman zaben ‘yan majalisar dokoki.
A Ghana, dai mutane 19,388 suka harbu da cutar ta korona, sai kuma 117 da cutar ta yi ajalinsu a cewar alkalumman kamfanin dilancin labaren AFP.
342/